Labarai
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar talata 21 ga watan agusta kuma laraba 22 a matsayin shagulgulan Sallah
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar talata 21 ga watan agusta kuma laraba 22 ga watan na agusta da muke ciki a matsayin ranar hutu domin gudanar da shagulgulan babbar Sallah.
Ministan cikin gida abdurrahman dambazau ne ya bayyana hakan da yammacin jiya cikin wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar cikin gidan dr muhammad umar ya fitar.
Abdurrahman Dambazau ya kuma kirayi al’ummar kasar nan da su yi amfani da lokacin hutun wajen nuna soyayya tsakanin al’umma da kuma nuna kishin kasa domin ciyar da kasar nan gaba.
Ya kuma bukaci al’ummar kasar nan da su ke ciki da wajen kasar nan, da su ci gaba da nuna goyon bayan su ga gwamnatin shugaba muhammadu buhari a kokarin da ya ke yi na wanzar da zaman lafiya a kasar nan.
Ya kuma yiwa al’umma fatan gudanar da shagulgulan sallah lafiya da komawa bakin aiki lafiya.