Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ranar ma’aikata: Gwamnati ta ayyana litinin 3 ga watan Maris a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 03 ga watan Mayu, a matsayin  ranar hutu a fadin kasar nan na bikin murnar ranar ma’aikata ta Duniya.

Ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola,ne ya sanar da hakan ga manema  labarai tare da godewa ma’aikatan kasar nan.

Ta cikin sanarwar da aka fitar yau Alhamis, da babban sakataren ma’aikatar Shuaibu Belgore ya fitar, Aregbesola, ya bukaci ma’aikatan da su kara jajircewa wajen gudanar da ayyukan su da gaskiya da zai bunkasa kasar nan.

Ministan ya kara da cewa, gwamnatin shugaba Buhari na yin duk mai yiwuwa wajen samarwa da ma’aikata kyakkyawan tsarin gudanar da aiki, ciki har da kyautata tsaro a fadin kasar nan don samar da ci gaba mai dorewa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!