Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudurin ta na cigaba da inganta harkokin kiwon lafiya a fadin Jihar.

Kwamishinan lafiya na Jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da wasu ayyuka biyu da suka hada da raba kayan aiki a babban asbitin garin Gwarzo tare da bude wata  akarantar Islamiyya.

Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya kara da cewa Gwamnatin Kano ta siyo kayayyakin aiki na Asbitin  da kudin sa ya kai Naira Millyan 70, don inganta harkokin kiwon lafiya a yankin.

Da yake bayani dangane da cutar kwalara da ta barke a jihar Kano,Kwamishinan yace Jihohi biyar ne Arewacin Kasarnan suka kamu da wannan cuta amma kawo yanzu gwamnatin ta dauki matakan gaggawa don magancesu.

Kwamishinan yayi kira ga al’umma dasu kula da tsafatar abinci da kuma mahllin su don gujewa barkewar cututuka.

A dai makwan da ya gabata ne muka kawo muku rahoto kan barkewar cutar kwalara a kananan hukumomin Gwarzo da Bebeji, yayin da aka sami rahoton mutuwar mutum 9 a karamar hukumar Gwarzo sai kuma mutum 10 a karamar hukumar Bebeji.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!