Labarai
Gwamnatin tarayya ta bada umarnin dawo da kudin London Paris club
Gwamnatin tarayya ta bada umarnin dawo da kudin London Paris Club da aka rabawa wasu Jihohi biyar na kasar nan da suka Dala biliyan 2 da miliyan 700, dai did a Naira biliyan 972.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da daukar matakin sai dai babu wani dalili da aka bayan na janye kudaden daga Jihohin Delta da Imo da Benue, sai Rivers da kuma Osun.
Sai dai kungiyar gwamnoni ta kasa ta kira wani taron gaggawa don kalubalantar wannan mataki da wasu daga cikinsu ke cewa akwai siyasa a ciki.
Tuni dai wasu gwamnonin ke cewa sun kashe kudin ta hanyar biyan albashin ma’aikata da kudin ariya, kamar yadda gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom ke fadi.
Samuel Ortom ya shaida cewa ya karbi naira biliyan 14 da miliyan 900, kuma ya biya bashin ‘yan fansho da garatuti da ariya, yayin da kwamishinan yada labaran Jihar Osun Adelani Baderinwa ke fadin basu da masaniyar janye kudin, wadanda kuma tuni suka kashe su.
Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari, ya bukaci yin ganawar gaggawar a yau Talata, da karfe 3 na rana a Sakatariyar kungiyar dake birnin tarayya Abuja