Labarai
Gwamnatin Tarayya ta bayar da hutun bikin ranar samun yanci

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu a fadin ƙasar domin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ƴancin kai.
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da ministan cikin gida Olibunmi Tunji-Ojo ya fitar, wadda a cikinta ya taya ƴan Najeriya murnar cimma wannan babban matsayi.
Ministan ya kuma buƙaci ƴan ƙasar su ci gaba da nuna kishin ƙasa da hadin kai da juriya, da ya ce su ke taimaka wa ƙasar wajen dunƙulewa waje guda ga mabanbantan kabilun ta tun lokacin samun ƴancin kai a 1960.
A ranar 1 ga watan Otoban 1960 ne dai Najeriya ta samu ƴancin kai daga Turawan mulkin Birtaniya da suka yi mata mulkin mallaka.
You must be logged in to post a comment Login