Labarai
Gwamnatin tarayya ta bukaci a mayar da ciyarwar alhazai zuwa jihohi
Gwamntain tarayya ta bukaci kasar Saudi Arebia da ta mayar da hidimar ciyar da Alhazan Najeriya ga kasar nan domin magance korafe-korafen da Alhazan ke kowacce shekara a lokacin aikin Hajji mai zuwa na shekar 2024.
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shattima ne ya bayyana hakan lokacin da tawagar hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON karkashin jagorancin shugabanta Barista Zikrullah Kulle Hassan suka kai ziyara domin gabatar masa da rahoton yadda aka gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023 da kuma shirye-shiryen aikin Hajjin bad’i ma shekarar 2024.
Yayin ziyarar tawagar hukumar NAHCON Mataimakin shugaban kasa Kashim Shattima yabawa da yadda NAHCON ta gudanar da aikin Hajjin 2023, har ma ya ce, mayar da harkokin ciyar da alhazai karkashin hukumar jindadin alhazan jihohi zai taimaka wajen inganta dandanon abincin wanda zai yi dai-dai da wanda suke ci da tare da kula da tsaftarsa yadda Alhazan zasu iya ci cikin kwanciyar hankali su kuma gudanar da ibadar aikn Hajjin cikin nutsuwa.
Kashim Shattima ya kuma bukaci shugabancin hukumar karkashin Barista Zikrullah Hassan da su cigaba da wayar da kan alhazan Najeriya sharadai da hukunce- hukunce da ka’idojin aikin Hajji domin hakan zai kara taimakawa maniyyatan yadda za su gudanar da aikin Hajjin kamar yadda addinin muslinci ya tsara, kamar yadda sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da Jama’a na Hukmar NAHCON Musa Ubana Dawaki ya fitar.
Da yake gabatar da rahoton Hukumar cikin harshen turanci Zikrullah Kunle Hassan ya bayyana nasarori da kuma kalubalen da NAHCON ta fuskanta a aikin Hajjin da ya gabata na 2023, har ma cikin harshen Hausa Kwamishina mai kula da harkokin kudi da ma’aikata da tsare-tsare na hukumar NAHCON Alhaji Nura Hassan Yakasai ya yi bayani a madadinsa.
Yayin ziyarar tawagar ta Kunshi daukacin kwamishinoni da sauran ma’aikatan Hukumar kula da aikin Hajjin ta Kasa NAHCON
Idan za a iya tunawa a ranar ashirin ga watan yuli Wannan shekara ta 2023 ne shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu, ya mayar da kula Hukamar karkashin kulawar ofishin mataimakin shugaban Kasa Kashim Shattima.
You must be logged in to post a comment Login