Connect with us

Labarai

Gwamnatin tarayya ta bukaci a sanya masu fassarar yaren kurame yayin gabatar da labarai.

Published

on

Gwamnatin tarayya ta umarci gidajen Talabijan da su yi biyayya ga umarnin hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC na samar da masu fassarar yaren kurame yayin da suke gabatar da labarai.

 

Ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Mohammed ne ya ba da umarnin a yau Litinin a birnin tarayya Abuja yayin ganawa ta musamman da jami’an Cibiyar masu bukata ta musamman ta kasa.

 

Ministan ya ce za a sanar da umarnin ga dukkan gidajen Talabijin na gwamnati da masu zaman kansu a gobe Talata.

 

Rahotanni sun bayyana cewa umarnin ya biyo bayan korafin da Babban Daraktan cibiyar masu bukata ta musamman Mista David Anyaele ya yi, da ke cewa ana nuna wa mambobinsu musamman masu lalurar “ji” wariyar launin fata musamman ta bangaren yada labarai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!