Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

 Zamu sasanta rikicin KAROTA da ‘Yan adaidata sahu – NLC

Published

on

Kungiyar kwadago ta kasa NLC reshen jihar Kano ta bukaci masu baburan adaidai ta sahu da su kwantar da hankalin su, domin kuwa kungiyar za ta shiga tsakani dan ganin an musu daidaito.

Shugaban kungiyar Kwamred Kabiru Ado Minjibir ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a yammacin nan.

Ya ce, Kuma ce idan har ta Kama su zauna ga gwamnan Kano Abdullahi Umar ganduje domin ganin an musu adalci zasu zauna dashi.

Kwamred Kabiru Ado Minjibir ya Kuma ce yajin aikin da matuka baburan adaidaita sahun ya taba kowa da kowa har ma da al’amuran yau da kullum.

A gobe Talata ne dai gamayyar kungiyoyin ma’aikatan jihar Kano za su zauna da shugabannin Yan adaida ita sahun domin ganin an shawo kan matsalar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!