Labarai
Gwamnatin tarayya ta ce dakarun sojin kasar nan za su shiga cikin tsarin Inshorar Lafiya ta kasa

Gwamnatin tarayya ta ce dakarun sojin kasar nan za su shiga cikin tsarin Inshorar Lafiya ta kasa, domin tabbatar da cikakkiyar kulawa da lafiya ga jami’an tsaro, iyalan su da kuma waɗan da suka yi ritaya.
Karamin Ministan tsaro Bello Matawalle ne ya bayyana hakan a Abuja a jiya Talata, yayin bikin cika shekaru 20 da haɗin gwiwar shirin kiwon lafiyar ma’aikatar tsaro da Walter Reed Army Institute of Research Africa.
Matawalle ya ce wannan mataki zai karfafa tsarin kiwon lafiyar rundunar tsaro ta kasa tare da tabbatar da cewa dakarun soji da iyalan su suna samun irin kariyar lafiyar da sauran ‘yan kasa ke samu.
You must be logged in to post a comment Login