Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar tsoffin sojoji tayi alkawarin karbo hakkin mambobin ta

Published

on

Kungiyar tsoffin sojojin sama dana kasa da ruwa ta kasar nan, wato  REMENAF ta sha alwashin  karbo hakkin  tsoffin sojin  da suka bautawa kasar nan hakkunan su  musamman ma wadanda suka rasu.

Babban jami’in kungiyar reshen jihar kano Bala Munzali ne,  ya bayyana wa tashar Freedom Radio hakan  a kan kalubalen da iyalan sojoji suke fuskanta da halin ni ‘ya su da suke shiga bayan kammala aiki.

Bala Munzali ya kara da cewa suna zargin tsohuwar kungiyarsu ta LEGION da gazawa wajen kwatarwa sojojin hakkin su da suka hadar da fansho  DA garatuti, hakan ta sa suka kafa wannan kungiya ta REMENAF.

A nasa bangaren shugaban shirin samar da inshorar lafiya sojoji na kasa mai kula da jihohin Kano da Jigawa Tanimu Umar,  yace tsarin zai tanadi kyakyawan shirin da zai taimakawa iyalan sojin ba tare da samun tsaiko ko nakasu ba.

Labarai masu alaka.

Rundunar sojin sama ta musanta kai hare-hare kan fararen hula a Zamfara

Jiragen yaki za su iso Najeriya -Rundunar sojan sama

Shi kuwa  mataimakin shugaban kungiyar reshen jihar Kano Abdukadir Sulaiman Gwarzo,  kokawa yayi kan yadda gwamnati ta gaza basu gudunmawa a matsayin su na wadanda suka hidimtawa kasar nan.

Kungiyar da shuwagabannin ta sun yi kira ga duk wani jami’in soja dake aiki da kuma wadanda suka yi ritaya da su  shiga tsarin inshorar lafiya don samun kulawa data dace, kamar yadda wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya ruwaito  mana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!