Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta ce kula da masu cutar zazzabin Lassa kyauta ne
Gwamnatin tarayya ta ce kawo yanzu kula da masu dauke da cutar zazzabin Laasa kyauta ne, yayin da ta yi kira ga al’umma da su yi watsi da duk wani jita-jita da ake yadawa kan wannan batun.
Wannan na kunshe cinkini sanarwar da babban jami’in dake kula da cibiyar dakile dukkanin cuttuka ta kasa Dr, Chikwe Ihekweazu ya fitar a karshen makon nan.
Dr. Chikwe Ihekweazu na maida martani ne kan wani rahoto da wata jarida ta buga cewa, musababin tsadar wajen kula da masu cutar ta Lasa ya samu asali ne kan yadda ake samun yawan mace-mace mata masu juna biyu a kasar nan.
Haka zalika babban jami’in ya ce gwamnatin tarraya ta tabbatar da cewar nau’in maganin nan na ‘’Ribavirin’’ wanda shi ne babban magani da ake baiwa masu dauke da kyauta ne a dukkannin sassan kasar nan.