Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

An kame wasu mutane 145 da zargin hadassa rikicin manoma da makiyaya

Published

on

Wata majiya daga fadar Gwamnati ta tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda ta kasa ta kama mutane 145 da ake zargin suna da hannu a rikicin manoma da makiyya a sassan kasar nan da suka hada jihohin Benue da Kaduna da Nasarawa.

An dai kama mutanen ne a tsakanin watan Janerun shekara ta 2016 kawo watan janerun wannan shekarar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya baiwa hukumomin tsaro umarnin da su kama dukkanin wadanda ake zargi na da hannu cikin rikicin.

Majiyar wacce ta nemi a sakaya sunan ta, ta bayyana cewar daga cikin wadanda ake zargin an gurfanar da mutum 124 a gaban kotu, a yayin da ake cigaba da gudanar da binciken  mutum 21 kuma suke jiran a gurfanar da su gaban kotu.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!