Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya ta ce kula da masu cutar zazzabin Lassa kyauta ne

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce kawo yanzu kula da masu dauke da cutar zazzabin Laasa kyauta ne, yayin da ta yi kira ga al’umma da su yi watsi da duk wani jita-jita da ake yadawa kan wannan batun.

Wannan na kunshe cinkini sanarwar da babban jami’in dake kula da cibiyar dakile dukkanin cuttuka ta kasa Dr, Chikwe Ihekweazu ya fitar a karshen makon nan.

Dr. Chikwe Ihekweazu na maida martani ne kan wani rahoto da wata jarida ta buga cewa, musababin tsadar  wajen kula da masu cutar ta Lasa ya samu asali ne kan yadda ake samun yawan mace-mace mata masu juna biyu a kasar nan.

Haka zalika babban jami’in ya ce gwamnatin tarraya  ta tabbatar da cewar nau’in maganin nan na ‘’Ribavirin’’ wanda shi ne babban magani da ake baiwa masu dauke da kyauta ne a dukkannin sassan kasar nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,336 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!