Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin titi na Naira biliyan 115 a Kano

Published

on

  • Aikin titin zai hadar da hanyar Kano zuwa Daura, zuwa Kongollam.
  • Wannan aiki za’a yishine duba da rashin girman haryar, tare da dakile hadduran da ake fama dashi.
  • A hannu guda Kuma kamfanin da zai gudanar da wannan aiki nuna farin cikinsa yayi na zamowa Wanda aka zaba don yin aikin.

Gwamnatin Nijeriya tace ta fitar da sama da Naira biliyan 115 domin yin aikin titin Kano zuwa Daura wanda zai kai har zuwa Kongollam daya haɗa jihohi 3.

Ministan ayyuka da gidaje Baba Tunde Fashola ne ya bayyana hakan a Yau yayin ƙaddamar da aikin na tsahon kilomita 132 a hanyar da ta haɗar da ta Kano, Jigawa da Kuma Katsina inda za’ayi gada har guda 3 akan hanyar.

Ministan ya kara da cewa ”wannan aikin za’a gudanar da shi ne sakamakon yadda hanyar ta kasance tayi ƙankanta da kuma yadda ake rasa rayuka akan titin.”

A nasa jawabin yayin ƙaddamar da aikin Ministan ruwa da more rayuwa Alhaji Sulaiman Adamu cewa yayi ‘wannan aikin yana da matukar mahimmanci sakamakon yadda hanyar take da manyan kasuwanni kuma akan samu yawan asarar rayuka.’

A gefe guda kuwa Abdussamad Isyaka Rabi’u BUE da ya sami wakilcin Alhaji Kabiru Rabi’u bayyana jindadin su suka nuna, tare da yabawa gwamnati, kasancewar kanfanin na BUE shine zai gudanar da aikin.

Freedom Radio ta rawaito cewa yayi ƙaddamar da aikin, ƙananan ministoci da masu riƙe da sarautun gargajiya ne suka samu halartar wurin.

Rahoton:Umar Abdullahi Sheka

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!