Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan sanda sun kama wasu matasa dayin dafara a Kano

Published

on

  • Rundunar ‘yan Sandan ta kama matasan biyu ne da shaidar wani gidan radiyo na bogi a nan Kano.
  • Wadannan matasan har ila yau tana zargin matasan da yin dafara .
  • Yanzu dai matasan na hannun Rundunar domin gudanar da bincike.

Rundunar ‘yan sandan a Jihar Kano ta samu nasarar kama wasu ‘yan Jarida na bogi suna damfarar mutane ta hanyar tura musu sakon karta kwana na karya.

Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ya bayyana hakan.

SP Kiyawa yace sun kama matasan su biyu da ake zargi dauke da katin shaidar wani gidan Radio mai zaman kansa a nan Kano lokacin da suka je wani shagon siyarda kaya suka tura musu Alert na karya

Matasan biyu da ake zarginsu suna damfarar mutane masu suna Mujahid Muhammad da kuma Abba Imam sun amsa zargin da ake musu.

Freedom Radio ta  ruwaito cewa rundunar ta ce ‘da zarar ta kammala bincike akan wadanda ake zargin nasu, zata gurfanar dasu a gaban kotu domin su girbi abinda suka shuka.

 

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!