Labarai
Gwamnatin tarayya ta kai karin kayan agaji ga mutanen Tudun Biri

Gwamnatin tarayya ta kai karin kayan agaji ga al’ummar garin Tudun Biri da ke jihar Kaduna, biyo bayan wani mummunan harin da jiragen yakin sojoji ya kai a watan Disamban shekarar 2023.
Babban hafsan soji GOC shiyya ta daya kuma kwamandan sashe na 1, rundunar hadin gwiwa ta Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Mayirenso Saraso, ne ya bayyana hakan a madadin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu.
Gwamnatin tarayya ta gabatar da babura guda biyu da injinan janareta na Kamfanin Corolla da na’urar amsa kuwwa guda biyu da kayan sauti da da manyan fitulu masu karfin Watt 500 inda aka raba su ga mutanen da suka hada da Isuwa Haruna da Ridwan Yakubu da Isah Ahmed.
Saraso ya ce, matakin ya yi dai-dai da shawarwarin da wata tawagar gwamnatin tarayya da ta ziyarci al’ummar bayan afkuwar lamarin.
You must be logged in to post a comment Login