Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnonin Arewa sun hada wa mutanen Tudun Biri tallafin miliyan 180

Published

on

Gwamnonin Arewacin Najeriya 19 sun amince su yi matsin lamba ga hukumomi don ganin an yi wa mutanen Tudun-Biri adalci bayan harin bam da sojojin kasar suka kai musu cikin kuskure a jihar Kaduna.

Kazalika gwamnoni sun yi kira da a gudanar da bincike kan lamarin, suna masu fatan wannan tsautsayin ba zai sake faruwa ba a Najeriya.

Shugaban Kungiyar Gwamnoni kuma Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya bayyana haka a wurin kaddamar da taronsu a wannan Juma’ar a jihar Kaduna.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin ya bukaci gwamnonin da su yi shiru na tsawon minti guda domin karrama mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyar harin na Tudun-Biri, yana mai cewa, kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu, nauyi da ya rataya a wuyen gwamnati.

Ya kuma jinjina wa gwamnatin tarayya kan yadda ta yi gaggawar mayar da martani jim kadan da faruwar lamarin.

A bangare guda, gwamnonin sun bai wa mutanen na Tudun-Biri tallafin naira miliyan 180.

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin sake gina garin karkashin wani shirinta na Fulako kamar yadda mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima ya bayyana a lokacin da ya ziyarci mutanen da harin ya rutsa da su a asibiti a jihar Kaduna.

Mutane daga ciki da wajen Najeriya sun yi ta kira da a biya mutanen diyyar kudade tare da bayyana fushinsu kan abin da suka kira sakaci da rashin kwarewar jami’an tsaron Najeriya wanda shi ne dalilin kaddamar da harin na kuskure kan mutanen da ke taron Maulidi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!