Labarai
Gwamnatin tarayya ta saki kaso biyu na sunayen wadanda suka sace dukiyar kasa
Gwamnatin tarayya ta saki kaso na biyu na sunayen wadanda ta ce sune suka sace dukiyar kasar nan tsawon shekaru goma sha shida da dawowar mulkin dimukuradiya a kasar nan.
Cikin wadanda ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammed ya ce sun yi wadaka da dukiyar Najeriyar sun hada da: tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro kanal Sambo Dasuki mai ritaya.
A cewar Alhaji Lai Muhammed, a binciken da hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta yi kan tsohon mai baiwa shugaban kasa shawarar kan harkokin tsaro, ta gano cewa, ba ya ga rabon sama da dala biliyan biyu da ya yi na kudaden makamai, Sambo Dasukin ya kuma yi almundahanar naira biliyan 126 da kuma dala biliyan daya da rabi da kuma fan miliyan biyar da rabi.
Ministan yada labaran, ya ce; bawai anan kawai barnar ta tsaya ba, a cewar sa, Itama tsohuwar ministar man fetur Diezani Allison Madueke, ta wawure naira biliyan 23, ba ya ga wata badakalar dala biliyan uku na kwantiragi a bangaren mai.
Haka zalika ministan ya ce; shima tsohon babban hafsan sojin kasa na kasar nan, laftanal janar Kenneth Minimah ya wawushe kusan naira biliyan goma sha hudu yayin da takwaransa wanda ya gabace shi, Janar Azubuike Ihejirika mai ritaya, aka kwato naira biliyan hudu da rabi da kuma wasu naira miliyan 29 daga gare shi.