Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da rufe makarantunta na sakandare

Gwamnatin tarayya ta sanar da umarnin rufe makarantunta na sakandare na makarantun hadaka da ake kira da Unity Colleges.
A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar a ranar Juma’a wadda daraktan makarantun sakandare, Binta Abdulqadir ta sanya wa hannu a madadin ministan ilimi Tunji Alausa, gwamnatin ta sanar a rufe kwalejojin guda 47 a faɗin kasar nan.
Sanarwar ta ce ma’aikatar ta ɗauki wannan matakin ne “saboda barazanar tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar, da kuma yunƙurin daƙile aukuwar wata matsala,” kamar yadda sanarwar ta nuna.
Ko da yake sanarwar ta yi nuni da cewa rufe makarantun na wucin gadi ne, sai dai ba ta sanar da ranar da za a buɗe su ba.
Kazalika ta kuma umarci shugabannin makarantun su tabbatar an aiwatar da umarnin.
You must be logged in to post a comment Login