Labarai
Gwamnatin tarayya ta sha alwashin kammala aikin titin Wuju-wuju shekaru 2

Gwamnatin tarayya ta ce, za ta kammala aikin titin Wuju-wuju cikin watanni 24.
Ƙaramin ministan ayyuka da gidaje, Yusuf Abdullahi Ata, ne ya bayar da wannan tabbaci bayan ƙaddamar da aikin titin a ranar Litinin.
Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta ware Naira Biliyan Arba’in da Bakwai don ganin an kammala titin wanda tsohon gwamna Kwankwaso ya fara yin shi a lokacin da ya ke kan mulki.
Haka kuma, Yusuf Ata ya ce, ya musanta Rahotonnin da ke cewa aikin haɗin gwiwa ne da Gwamnatin jihar Kano.
Ministan, ya kuma bayar da tabbacin ci gaba da biyan diyyar waɗanda aikin ya shafa.
You must be logged in to post a comment Login