Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da mutuwar shugaban kungiyar ISWAP  Malam Baƙo

Published

on

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da mutuwar magajin shugaban kungiyar ISWAP Malam Bako.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro manjo janar Babagana Mongonu ya tabbatar da mutuwar sa.

Mongonu ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labaran fadar shugaban kasa bayani jim kadan bayan kammala wata ganawa kan sha’anin tsaro jiya a fadar shugaban kasa.

Ya ce, Malam Bako shi ne magajin Abu-Mus’ab Albarnawi wanda ke rikon mukamin shugaban kungiyar ISWAP.

A cewar sa, Bako ya mutu ne adaidai lokacin da yake tare da jiga-jigan mambobin kungiyar.

Wannan na zuwa ne sama da mako guda bayan da babban hafsan tsaron kasar nan Janar Lucky Irabor ya tabbatar da mutuwar tsohon shugaban kungiyar ISWAP Abu Musab Al-Barnawi.

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!