Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Gwamnatin Tarayya za ta dage dokar hana magoya baya shiga kallon wasanni – Dare

Published

on

Ministan Matasa da Wasanni, Sunday Dare, ya ce kwanannan za a dage dokar hana ‘yan kallo shiga filin wasa da Kwamitin Gwamnatin Tarayya kan yaki da cutar Corona ya sanya a Najeriya.

Dare ya bayyana haka ne a ranar Talata 29 ga watan Yuni yayin wata ziyara da ya kai wa sansanin Super Eagles rukunin B da ke Abuja.

Yanzu haka dai ‘yan wasan na shirye-shiryen buga wasan sada zumunci na kasa da kasa da Mexico a ranar Lahadi 4 ga watan Yuli a Amurka.

“Muna fatan ganin magoya bayanmu sun dawo ci gaba da shiga kallon wasanni a filayen wasa da zaran mun tabbatar matakan dakile yaduwar cutar COVID-19,” in ji Dare.

Ministan ya kara da cewa, “Magoya baya suna da matukar mahimmanci ga wasanni, saboda haka za mu sanya ido kan lamarin sannan mu yi aiki tare da hukumomin da abin ya shafa don aiwatar da hakan.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!