Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Ministan Wasanni ya bukaci NFF ta yiwa Gernot Rohr jan kunne

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta umarci Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya da ta yi kira ga mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Gernot Rohr, wajen tabbatar da gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

Ministan Matasa da Wasanni Sunday Dare, ya ce, ya yi mamakin da Rohr bai kasance tare da tawagar Super Eagles da ke gida ba, a lokacin da ya ziyarci sansanin ‘yan wasan dake Abuja.

Ya kuma ce, ko alama bai ga dalilin da zai sa Rohr ya nuna bambanci ga ‘yan Najeriya wajen horar da ‘yan wasan Super Eagles na gida da na waje ba.

‘Yan Najeriya ne suka dauki Gernot Rohr aiki, saboda haka, bai kamata ya nuna wariya ga ‘yan wasan Super Eagles na gida da wadanda ke kasashen waje ba, domin kowane na nuna bajinta sosai, dole ne a girmama su kuma a kula da su.

“Ya zama dole NFF ta kira shi don ta ba shi umarni kuma ya tabbatar da yin biyayya ga yarjejeniyar kwantiragin da ya sanya hannu da Najeriya,” in ji Dare.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!