Labarai
Gwamnatin tarayya za ta fara yin gwajin tu’ammali da ƙwaya ga wadanda za ta dauka aiki

Gwamnatin tarayyar Najeriya, ta ce, za ta ɓullo da shirin yin gwajin miyagun ƙwayoyi ga masu neman aikin gwamnati, ta na mai cewa, daga yanzu za a saka gwajin ta’ammali da ƙwaya a cikin abubuwan da suka zama dole kafin a ɗauki mutum aiki.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen ya fitar.
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumomin ƙasar nan za su haɗa hannu da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi wato NDLEA ne domin samun nasarar wannan aikin.
Ya ƙara da cewa ɗaukar wannan matakin ya zama dole ne bayan yawaitar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, musamman a tsakanin matasa.
You must be logged in to post a comment Login