Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Gwamnatin tarayya za ta ginawa ɗaliban BUK gadar sama

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce za ta ginawa ɗaliban jami’ar Bayero gadar sama da za su riƙa tsallakawa domin rage yawan samun haɗarurruka yayin tsallaka titi.

Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola ne ya bayyana hakan lokacin da yake buɗe aikin wani titi mai nisan kilo mita ɗaya da digo biyar da gwamnatin tarayya ta samar a jami’ar ta Bayero.

Ministan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatar ayyuka na ƙasa reshen jihar Kano Injiniya Yahaya Baba Ali, ya ce yanzu haka gwamnati ta fara samar da manyan hanyoyin zirga-zirgar ababen hawa masu inganci a manyan makarantun ƙasar nan domin ƙara inganta harkokin koyarwa da kuma kiyaye rauwar ɗalibai.

Tun da fari dai jami’ar Bayero ita ce ta kai kokenta ga gwamnatin tarayya kan barazanar da ɗalibai suke fuskanta a yayin tsallakawa titi, inda ta bukaci  da a samar da gadar da za ta sauƙaƙawa ɗaliban zirga-zirgar su.

Ko da yake nasa jawabin shugaban Jami’ar Bayero Farfesa Sagir Adamu Abbas ya yabawa gwamnatin bisa yadda ta karbi koken da suka shigar mata musamman na lalacewar wasu daga cikin hanyoyin sufuri na jami’ar wanda kuma ta fara gyara su tare da samar da wasu.

Sagir Adamu Abbas ya ce a yanzu haka gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da samar da hanyoyin sufuri a jami’ar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!