Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Tarayya za ta kashe fiye da Tiriliyan 6 a tallafin Fetur- El-rufa’i

Published

on

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’I ya ce, gwamnatin tarayya za ta kashe sama da naira tiriliyan shida a matsayin kudin da za ta bayar na tallafin man fetur a cikin watanni shida na wannan shekarar da muke ciki.

El-Rufa’I ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya karo na 12 wanda aka gudanar a jihar Kaduna.

Gwamnan ya kuma kara da cewa, za’a sake kashe kimanin naira tiriliyan hudu a matsayin kudin tallafin Naira, haka kuma Najeiya za a kashe kimanin biliyan dari uku a matsayin kudin tallafi a bangaren hasken wutar lantarki.

El-Rufa’i ya kuma zargi kamfanin NNPC da cewa bai sanya ko sisi ba a asusun gwamnatin tarayya na rabin shekarar 2021 da ta gabata, wanda hakan yasa Najeriya ta dogara da kudaden da take samu daga ketare da kuma kudaden harajin cikin gida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!