Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin da zai shawo kan wahalar fetur cikin gaggawa

Published

on

Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin mutane goma sha hudu da zai gaggauta kawo karshen matsalar karancin man fetur din da ake fama da shi a fadin Najeriya.

Hakan na dauke ne ta cikin wata sanarwa da daraktan hukumar rarraba albarkatun kasa da ayyukan more rayuwa da kuma adanawa Ogbugo Ukoha ya fitar a jiya Talata lokacin da yake wata ganawa da masu ruwa da tsaki kan harkokin man fetur.

Ogbugo ya ce, sabon tsarin da za su gudanar a yanzu zai taimaka wajen saukaka karancin mai da ake fama da shi a wasu sassa.

Haka kuma ya ce, za su hada kai da wasu hukumomi don magance wannan matsala.

Ogbugo Ukoha kuma kara da cewa, dokar hukumar a cikin sashi na 181 ya basu damar kirkiro da sabbin dabaru musamman yadda za’a rika tsara rabon albarkatun kasa, ciki har da man fetur domin ganin man ya isa zuwa kowane bangare.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!