Connect with us

Kiwon Lafiya

Majalisar zartarwa ta amince da kashe biliyan 27 a ayyukan raya kasa

Published

on

 

Majalisa zartaswa  ta amince da fitar da Naira Billiyan 27 don sayan buhu-hunan Gero da kayayaykin wuta lantarki da kuma gyara wasu daga cikin Titunan Birnin tarayya Abuja.

Ministan Noma da albarkatun kasa Audu Ogbeh ne ya bayyana haka, a zaman majalisar na jiya, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Audu Ogbeh  ya kuma ce, an ware Naira Billiyan Tara da milliyon hudu da nufin sayan Gero tan Dubu sittin  baya ga amince da sayan tan din Masara Dubu sitin da daya da Dawa da kuma Ridi, don samar da iri da za a suka a damar bana.

A nasa banagaren Ministan wutan lantarki da gidaje   Babatunde Raji Fashola ya ce majalisar ta kuma amince da fitar da Naira Biiliyon Bakwai da Milliyon daya, don gyara titin Abaji mai hannu biyu da wata gada, duk a  birnin tarraya Abuja don saukaka masu ababen-hawa zirga-zirga.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,336 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!