Labarai
Gwamnatin tarayyar ta ware ranar Litinin a matsayin ranar hutu
Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ayyana ranar Litinin 2 ga watan Oktoba 2023 a matsayin ranar hutu a fadin Kasar, don bikin ranar samun ‘yancin kan Nijeriyar.
Ministan cikin gida na kasar Olubunmi Tunji Ojo ne ya sanar da hakan a yau Alhamis, a babban burning tarayya Abuja yayin taya kasar murnar cika shekara 63 da samun ‘yancin kai a madadin Gwamnatin tarayyar.
Da ya ke bayani ta bakin babban sakataren ministan cikin gidan, Oluwatiyin Akinlade cewa yayi, ‘ministanbua tabbatar da cewa tana nan tana tanade-tanadan da zai kawo karshen matsalar matsalar da al’ ummar kasar ke ciki’.
Wanda ya ce ‘gwamnati na sane da wahal-halun da matsin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta, da Kuma karancin tsarin da duniya ke ciki, Wanda har ita Nijeriya ba’a barta a baya ba, da suke sa ran nan bada jimawa ba zasu kawo karshen ta’.
You must be logged in to post a comment Login