Labarai
Gwamnatin Yobe ta ware miliyan 389 domin ciyarwar Azumi

Mai Mala Buni ya amince da Naira miliyan 398 don ciyarwar Ramadan a Yobe State
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da kashe sama da naira miliyan 398 domin gudanar da shirin ciyarwa da Tafsiri na watan Ramadan na shekarar 2026 a fadin jihar. Ma’aikatar Harkokin Addini da Kyautata Tarbiyya ta jihar ce za ta aiwatar da shirin, da nufin tallafa wa marasa galihu a watan azumi.
Domin fadada shirin, gwamnatin ta kara yawan cibiyoyin ciyarwa daga 101 a bara zuwa 130 a kananan hukumomi 17 na jihar. A tsarin da aka tsara, kowace cibiya za ta rika samar da abincin buda baki ga mutane 100 a kowace rana, lamarin da ake sa ran dubban jama’a za su amfana da shi.
Bayanin rabon kudin ya nuna cewa sama da naira miliyan 338 za a kashe wajen sayen raguna da kayan hadin girki, yayin da aka ware naira miliyan 60 domin alawus ga malaman addini da za su jagoranci Tafsiri. Haka kuma, an amince da rabon buhunan shinkafa 2,300 da galan 400 na man girki ga cibiyoyin 130 domin saukaka aiwatar da shirin.
Da yake jawabi a wurin kaddamar da rabon kayan a Damaturu, Kwamishinan Harkokin Addini da Kyautata Tarbiyya, Yusuf Umar, ya yaba wa gwamnan bisa dorewa da fadada shirin, yana mai cewa hakan na nuna jajircewar gwamnati wajen kula da marasa galihu a watan Ramadan. Ya kuma gargadi kwamitocin da ke kula da cibiyoyin da su guji karkatar da kayan, yana mai jaddada cewa ba za a lamunci almundahana ba.
You must be logged in to post a comment Login