Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Yadda yara masu karancin shekaru ke hawa Babura da ake kira da Roba-roba a Kano

Published

on

Daga Mu’azu Tasi’u Abdurrahman

Wani sabon al’amari da a iya cewa ba a saba gani ba, shi ne yadda ake ganin masu Babura masu kafa biyu wanda ake yiwa lakabi da roba-roba na baiwa kananan yara suna tukawa da sunan koyo.

Wannan lamari dai ana yin sa ne da nufin haya ta yadda yaran kan biya wasu kudade kafin a ba su babur din da kuma lokacin da za su dawo da shi.

Babbar damuwa kan wannan lamari bai wuce ganin yaran a manyan tituna da lunguna suna guje-guyje wanda hakan ke zama barazana ga lafiya yaran.

A zantawa da wasu daga cikin yaran don sanin cewa ko iyayensu sun san suna hawa kan baburan, sun bayyana mana cewa yawanci ba a san suni ba, kawai dai sukan kirkiri wurin da za su je ne ko kuma su yi ta zagaya unguwar da suke ciki da nufin koyo.

Mazauna birnin Kano da dama sun bayyana mutukar takaicinsu kan yadda wannan dabi’a take neman zama barazana ga lafiya da kuma dukiyoyin al’umma,

Kazalika sun kuma nemi daukin hukumomin da abin ya shafa kan su kawo musu dauki kan wannan lamari.

Umar Yusif wani matashi ne da yake aiwatar da wannan sana’a a unguwar Kofar Dawanau ya bayyana cewa sun kirkiro wannan sabuwar hanyar neman kudi ne da nufin nemawa kansu madogara sakamakon matsalar tattalin arziki dake addabar al’umma a wannan lokaci.

To ko hukumar dake bayar da lasisin tuki ta jihar Kano sun san da wannan batu?

Babban daraktan hukumar Garba Abdullahi Gaya ya bayyana cewa baiwa wani abin hawa da zummar karbar kudi Awa-awa haramtacciya ce kuma ta saba da dokokin hukumar su.

Har Ila yau, Garba Abdullahi ya ce hukumarsu zata gurfanar da duk wani karamin yaro da ta kama a kan titi yana tuka abin hawa ba bisa ka’ida ba a kotun yara dake nan Kano.

Nabulisi Abubakar Kofar na’isa shi ne kakakin hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano (KAROTA) ya bayyana cewa sashi na biyu na dokar hukumarsu da aka samar a shekarar 2012 ta sanya tarar dubu 20 ko zaman wata shida a gidan gyaran hali.

 

Kakakin ya kuma yi kira ga al’umma musamman iyaye kan su kara sanya idanu a kan ‘ya’yansu don gudun fadawa mawuyacin hali a nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!