Connect with us

Jigawa

Majalisar Jigawa ta bada aikin kwangilar matatun ruwa

Published

on

Majalisar zartaswa ta jihar Jigawa ta bada kwangilar gina sababbin matatun ruwa guda shida akan kudi naira miliyan 173.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Bala Ibrahim ne ya bayyana yayin zantawa da manema labarai a bayan kamala taron majalisar zartarwa ta jihar a yau alhamis a birnin Dutse.

Bala Ibrahim ya ce, majalisar ta amince da bada aikin domin kara inganta ruwan sha a wasu garuruwan da ke fama da karancin ruwan sha a jihar.

Kwamishinan ya kara da cewa garuruwan da zasu amfana da aikin ruwan sun hada Basirka, Sabon-Garin-‘yaya’, da Bosuwa, Dakaiyawa, Gidan Lage, da Dangyatun, Maimazari da kuma Sabongarin Birnin Kudu.

Ya kara da cewa majalisar zartarwa ta kuma amince da gina sabbain matatun ruwa a garin Kila, Jigawar-Marka, Kunkuru, Garkon-Alli da kuma Dan Faramtama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!