Labarai
Gwamnonin Arewa maso gabas sun buƙaci shugaba Tinubu ya fifita aikin haƙar fetur a yankin

Gwamnonin yankin arewa maso gabashin kasar nan sun buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya fifita komawa aikin haƙar man fetur a rijiyoyin Kolmani da na yankin tafkin Chadi a wani ɓangare na yunƙurin farfaɗo da tattalin arziki da rage matsalar tsaron yankin.
Gwamnonin sun bayyana hakan ne a lokacin da suka ziyarci shugaba Tinubu a fadar mulki ta Villa da ke birnin tarayya Abuja.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, wanda ya yi magana a madadin gwamnonin, ya ce komawa aikin haƙar man yankin zai taimaka wa ayyukan soji a yankin tare da buɗe ƙofar ayyukan ci gaba a yankin.
Zulum ya yaba wa Shugaba Tinubu kan ci gaba da yaƙi da Boko Haram tare da bayar da tallafi ga iftila’in ambaliya da ya auku a jiharsa a shekarar da ta gabata.
You must be logged in to post a comment Login