Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

CNF tasha alwashin gurfanar da Gwamnatin tarayyar a Kotu kan kisan da sojoji sukayi a Kaduna

Published

on

Kungiyar ‘Concerned Northern Forum’ da lauyoyi suka kafa, ta sha alwashin gurfanar da gwamnatin tarayya a gaban kotu, inda ta bukaci a biya diyya ga Iyalan wadanda harin bam na garin Tudun Biri dake karamar hukumar igabi a jihar Kaduna ya rutsa da su .

Da yake jawabi a madadin kungiyar lauyoyin, Barista Nafi’u Abubakar, ya bayyana cewa kungiyar zai tabbatar da cewa iyaye da yan uwan wadanda aka babu gaira babu dalili an yi musu adalci yadda ya kamata.

 

Nafi’u wanda ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna a ranar Asabar, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa don tabbatar da gudanar da cikakken bincike kan wannan lamari.

 

Ya zuwa yanzu an gano cewa an kashe mutanen kauyen sama da 120 yayin da suke gudanar da bikin Mauludi a daren Lahadin da ta gabata.

 

Yace ya zama wajibi a hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika, sannan a samar da matakan hana sake afkuwar irin haka a nan gaba.

 

“Muna kuma kira ga rundunar sojin Najeriya da ta sake duba ka’idojin aiki tare da horar da jami’anta, domin gujewa asarar rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba yayin ayyukan soji. Yana da matukar muhimmanci rundunar sojojin Najeriya a matsayinta na mai kare kasa, ta yi taka-tsan-tsan don gujewa sake samun barnar da aka samu da kuma asarar rayukan fararen hula,” inji shi.

 

Kungiyar mai dauke da mambobi sama da 600 sun mika sakon ta’aziyya ga iyalai da yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan lamari.

 

“Mun tsaya mu su akan wannan abun mara dadi da ya faru har sai mun ga anyi musu adalci. Kungiyar ‘Concerned Northern Lawyers Forum’ za ta yi aiki tukuru wajen neman hanyoyin da doka ta tanada domin neman diyyar rayukan wadanda abun ya shafa,” inji shi.

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!