Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan Jarida biyu a Kano sun lashe lambar yabo ta shekara

Published

on

Yan jarida biyu daga jihar Kano Shehu Usman Salihu na Premier Radio da Jamila Siyoji Adam ta Arewa Radio, sun lashe lambobin yabo na gwarzon shekara ta bana a ɓangaren gabatar da shirye-shirye da karanta labarai.

Shehu Usman Salihu na premier Radio shi ne ya lashe zaɓen gwarzon mai gabatar da shirye-shirye a ɓangaren maza , yayin da Jamila Siyoji Adam ta Arewa Radio ta lashe zaben gwarzuwar shekara a ɓangaren Karanta labarai a Shekara ta 2023 a ɓangaren mata.

Wata kungiya ce mai suna Nigerian Radio Award ta shirya Inda yan jaridu daga sassa daban-daban na Nigeria suka shiga gasar Kuma aka yi ta zabe har Allah ya bada nasara ga yan jaridun jihar kano biyu suka lashe zabukan.

Dama dai duk shekara kungiyar ta kan shirya irin wannan zabe Inda ake bada dama ga mutanen gari su zabi wadanda suka shiga zabe ta hanyar yanar gizo a ɓangarori daban-daban na aikin Radio

Taron da aka gudanar jiya a Abuja ya sami halartar yan jaridu da dama daga sassa daban-daban na Nigeria.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!