Labarai
Gwamnonin arewa sun yiwa gwamnan jihar Kwara ta’aziyyar rashin mahaifinsa
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2020/07/Kwara-State-Governor.jpg)
Kungiyar gwamnonin arewacin kasar nan sun nuna alhinin bisa rasuwar mahaifin gwamnan jihar Kwara Abdurrahman Abdurrazak wato Alhaji Abdulganiyyu Folorunsho Abdurrazak mai darajar SAN wanda ya rasu a daren Asabar.
Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Plateau Simon Lalong ne ya aike da ta’aziyyar ta hannun daraktan yada labarai na kungiyar Dakta Makut Macham a yau Asabar.
Sanarwar ta bayyana rasuwar Alhaji Abdulganiyyu Abdaurrazak a matsayin rashi babba a kasar nan kasancewar sa mutum na farko a arewa da ya taba zama lauya kuma mai lambar kwarewa ta SAN a don haka babban rashi ne ga al’ummar jihar Kwara da ma kasa baki daya.
Kazalika sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin wanda ya sadaukar da rayuwar sa wajen hidimtawa al’umma a lokacin rayuwar sa wanda baza a manta da rashin sa ba tsawon rayuwa.
You must be logged in to post a comment Login