Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jirgin kasa zai ci gaba da sufuri tsakanin Kaduna zuwa Abuja

Published

on

Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya ce za a dawo a ci gaba da sifirin jirgin kasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna a ranar 29 ga watan Yulin da muke ciki.

Amaechi ya bayyana hakan ne lokacin gwada wasu sabbin taragun jirgi da za su rika zirga-zirga tsakanin Kaduna zuwa Abuja a yau Asabar.

An dai tsaida aikin ne a watan Maris din bana da ya gabata a wani mataki na dakile annobar cutar COVID-19.

A cewar Ministan, dimbin al’umma daga bangarori daban-daban ne suka bukaci da a dawo aikin kafin Sallar layya ta makon nan.

Ministan ya jaddada cewar, tuni gwamnati ta dauki matakan dakile yaduwar annobar cutar a wannan lokacin a bangarorin sufurin jiragen kasa.

Shugaban kamfanin sufurin jiragen kasa na kasa Fidet Okhiria ya ce aikin sufurin zai dawo gadan-gadan a Larabar makon nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!