Labarai
Gwamnonin kudu maso kudanci sun bukaci a basu kaso 13 na kudin sayo makamai
Gwamnonin kudu maso kudancin kasar nan sun bukaci gwamnatin tarayya da ta biya su kaso 13 cikin 100 na kudaden da ta ware domin sayo makamai.
Gwamnonin sun dau wannan mataki ne yayin wani taro da suka gudanar a garin Fatakwal da ke jihar Rivers.
Wadanda suka halarci taron sun hada da: Nyeson Wike na jihar Rivers da Ifeanyi Okowa na jihar Delta da Seriake Dickson na jihar Bayelsa da Udom Emmanuel na jihar Akwaibom da kuma mataimakin gwamnan jihar Edo Phillip Shuaibu.
A wata sanarwar bayan taro da gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya karantawa manema labarai, ta ce; gwamnonin suna bukatar a ware musu kaso goma sha uku cikin dala biliyan daya na kudaden da aka ware domin sayo makamai, kamar yadda aka saba basu a rabon arzikin kasa.
Cikin sanarwar dai gwamnonin sun kuma ce har yanzu suna kan bakar su wajen goyon bayan masu kiraye-kirayen sake fasalta kasar nan musamman wajen mai do da kasar nan tsarin larduna.