Labarai
Gwamnonin PDP sun amince Tanimu Turaki a matsayin ɗan takarar shugaban kasa a 2027

Gwamnonin jam’iyyar PDP na arewacin Najeriya, sun amince da tsohon Ministan Harkokin Shari’a, Alhaji Tanimu Turaki, a matsayin ɗan takarar da suke goyon baya a zaben shugaban kasa na jam’iyyar mai zuwa.
Wannan matsaya ta fito ne bayan taron da gwamnonin yankin suka gudanar, inda suka jaddada bukatar su hada kai domin tabbatar da cewa yankin Arewa ya samu cikakken wakilci a cikin jam’iyyar.
Wasu daga cikin gwamnonin sun bayyana cewa Tanimu Turaki mutum ne mai kwarewa da gogewa a harkokin mulki, kuma yana da nagartar da za ta iya hada kan mambobin jam’iyyar PDP a fadin kasa.
You must be logged in to post a comment Login