Labaran Kano
Gwmanatin kano ta kafa kwamitin wayar da kan a’lumma dangane da kidaya
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da kwamitin da zai wayar da Kan jama’a game da Muhimmancin kidayar da za a gudanar a fadin Kasa baki daya.
Da yake kaddamar da kwamitin a Ofishin sa a madadin Gwamnan Kano Sakataren Gwamnatin Alhaji Usman Alhaji Wanda shi ne shugaban kwamitin ya bayyana cewa kwamitin zai yi amfani da kafafen yada labari da guraren taron jamma’a don tabbatar da nasarar kidayar.
Alhaji Usman Alhaji yace sanin yawan al’umma abune mai mahimmanci wanda ta nan ne za a iya tsara duk wani abun more rayuwa da gwmanati take son yiwa al’ ummar ta.
Rahoto Abba Isah Muhammad
You must be logged in to post a comment Login