Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarki Aminu Ado Bayero ya sake nada sababbin Hakimai 4

Published

on

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Ya sake nada wasu sababbin Hakimai guda hudu tare da daga darajar wasu Hakimai guda shida.

Da yake jawabi lokacin da aka nada Hakiman, Mai Martaba Sakin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce, an nada su sarautun ne bisa cancanta da irin gudunmawar da suke bayar wa a cikin al’umma.

Sababbin Hakiman sun hada da;  Alhaji Nura Sunusi a matsayin Dan Darman Kano da Alhaji Sarki Hamidu Bayero a matsayin Barayan Kano da Alhaji Sayyadi Muhammad Yola a matsayin Fagacin Kano da kuma Alhaji Bello Idi a matsayin Kaigaman Kano.

Sai kuma Hakiman da aka ciyar da su gaba da suka hada da; Malam Umar Sunusi Bunun Kano da aka mayar da shi Dan Makwayyon Kano da Malam Ibrahim Hamza Bayero Dan Madamin Kano da ya koma matsayin sabon Dan Ruwatan Kano da Malam Lamido Abubakar Bayero Yariman Kano inda ya zama sabon Bunun Kano.

Sauran su ne; Alhaji Aminu Ahmad Sadiq Zamnan Kano zuwa Dan Madamin Kano da Alhaji Magaji Galadima Kachallan Kano zuwa Maga-yakin Kano da kuma Alhaji Bello Habibu Dankadai Fagacin Kano zuwa katikan Kano.

Mai Martaba Sarkin na Kano ya umarci hakiman da aka nada su zamo jakadu nagari a duk inda suka samu kansu tare da gudanar da aikinsu bisa gaskiya da rikon amana.

 

Rahoton: Shamsu Dau Abdullai

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!