Kiwon Lafiya
Gwmantain tarayya ta bukaci dakatar da dokar haramta kiwo barkatai
Gwamnatin tarayya ta bukaci da a dakatar da dokar nan da ta haramta yin kiwo barkatai da wasu jihohin kasar nan suka kafa.
Ministan tsaro Burgediya Janar Mansur Dan-Ali mai ritaya ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala wani taron sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar a fadar Asorok da ke Abuja.
A cewar sa dakatar da dokar a yanzu za ta taimaka gaya wajen dakile wasu matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan.
Ministan ya kuma bukaci jami’an tsaro da su gaggauta gurfanar da wadanda aka kama suna da hannu cikin rikicin da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma gaban kotu.
Da yammacin jiya ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wani taron sirri da shugabannin hukumomin tsaron kasar nan a fadar Asorok.