Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Haƙiƙanin abin da ya faru tsakanin Doguwa da Aruwa

Published

on

Shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya Alasan Ado Doguwa yayi wancakali da Kakakin jam’iyyar APC na Kano Ahmad S. Aruwa.

Lamarin ya faru ne yayin wani taron jam’iyyar inda Alasan Ado Doguwa ya gabatar da mahaifiyarsa ya bayyana cewa ita ce sirrin nasararsa a rayuwa.

Doguwa ya ce, biyayyarsa ga mahaifiyarsa ta sanya yake samun nasara a kan duk abin da ya sanya a gaba.

Ana ganin yayi hakan ne don martani da gugar zana, biyo bayan rikicinsu da mataimakin ɗan takarar Gwamnan APC Murtala Sule Garo.

A nan ne Aruwa ya yi ƙoƙarin zuwa wajen, a nan ne kuma Alasan Ado ya bi shi da mahangurɓa har ta kai sai da ƙyar aka ƙwace shi daga hannunsa.

Freedom Radio ta tuntuɓi Aruwa, ya ce, ya shigar da ƙarar Doguwa ga Gwamna Ganduje.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!