Labarai
Hakimin da aka yi garkuwa da shi a Neja ya shaƙi iskar ƴanci
Rundunar ƴan sandan jihar Neja sun ceto hakimin garin Wawa a ƙaramar hukumar Borgu Dakta Mahmud Aliyu da ƴan bindiga suka yi garkuwa da shi.
Mai magana da yawun rundunar DSP Wasi’u Abiodun ne ya tabbatar da kuɓutar ta sa.
Ya ce, an ceto shi ne a ranar Juma’a bisa ƙoƙarin da ƴan sanda sojoji da kuma bijilanti suka yi.
Hakimin ya kwashe mako guda a hannun waɗanda suka yi garkuwa da shi, sai dai tuni an miƙa shi zuwa asibiti don samun kulawa.
You must be logged in to post a comment Login