Connect with us

Addini

Hakuri shi ke inganta zamantakewar aure – Sheik Ali Yunus

Published

on

Limamin masallacin Juma‘a na Usman bin Affan dake Gadon Kaya Sheik Ali Yunus ya ce, babban abunda ke taka rawa wajan inganta aure shi ne hakuri da juriya, baya ga inganta zamantakewar juna.

Limamin ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan gidan Rediyo Freedom da ya gudana a yau, yana mai cewa, mafi yawan lokuta abunda da ke janyo lalacewar aure shi ne, rashin kai zuyciya nesa da wasu daga cikin ma’auratan ke yi.

Malamin ya kuma ce, rashin ilimin zamantakewar aure shi ma yana taka rawa wajen lalacewar auren wannan lokacin
Sheik Ali ya kuma ce, kamata ma’aurata su daina zargin junan su, sannan su rubanya kokarin sun a son kyutatawa juna.

Limami ya kuma yi kira ga ma’aurata da su rungumi dabi’ar yin hakuri da juriya don kaucewa bacin rana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,772 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!