Connect with us

Labarai

Gobe laraba ta zamo ranar tunawa da yin katin shidar ‘yan kasa – Pantami

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba sha shida ga watan Satumba a matsayin ranar yin  katin shidar ‘yan kasa  da nufin tallafawa ‘yan Najeriya su mallaki katin zama dan kasa a Najeriya.

Ministan sadarwar zamani Dakta Isah Ali Ibrahim Pantami ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da mai magana da yawun ministan Mrs Uwa Sulaiman ta fitar a yau Talata.

Ta cikin sanarwar Dakta Isah Fantami ya jaddadawa ‘yan kasar nan mahimmancin mallakar katin dan kasa inda ya ce, za su ci gaba da kyautata hanyoyin samar da katin ga kowanne dan kasa.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, za a gudanar da bikin bana ne ta kafar Internet, yana mai cewa, katin zama dan kasa na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arziki kasa da kuma kariya ga yan kasa a duk inda suka tsincisu kansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,771 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!