Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Halin da ‘yan gudun hijira ke ciki a fadin duniya

Published

on

Hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan rabin ‘yan gudun hijira a fadin Duniya yara ne kanana.

majalisar na bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a wani bangare na bikin tunawa da ranar ‘yan gudun hijira.

Wani rahoto da hukumar ta fitar abu na farko, ya nuna cewa akwai mutane miliyan 70.8 a fadin duniya da yake-yake ya tilastawa barin muhallansu, wanda ta ce ya zarce na mutanen da yakin duniya na biyu ya daidaita.

Abu na biyu shine, daga cikin wadanda yaki ya tilastawa barin gidajensu, akwai ‘yan gudun hijira miliyan 25.9, akwai kuma miliyan 41.3 da ke gudun hijira a kasashensu, sai kuma masu neman mafaka da ke jiran a basu takardar shaidar gudun hijira a wasu kasashen su miliyan 3.5.

Abu na uku ya nuna cewa sama da rabin ‘yan gudun hijira miliyan 25.9 da ake da su a fadin duniya yara ne ‘yan kasa da shekara 18.

A cewar hukumar UNHCR abu na hudu shine ya zuwa watan Mayu 2020, akwai masu neman mafaka miliyan 2.2 daga kasar Sudan ta Kudu kadai.

A kowacce dakika akan tilastawa mutum guda barin muhallinsa saboda rikice-rikice.

Kimanin kashi 25 cikin 100 na mutanen da suka rasa muhallinsu mata ne, inda kashi hudu daga cikin su mata ne masu juna biyu.

Kusan kashi 70 cikin 100 na ‘yan gudun hijira na rayuwa ne cikin tsananin talauci.

Kasashe masu tasowa na da kaso 80 na ‘yan gudun hijirar da suka tserewa yake-yake.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!