Connect with us

Coronavirus

Mai Corona daya ne ya rage a jihar Jigawa

Published

on

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya ce an rufe daya daga cikin cibiyoyin killace masu fama da cutar korona dake fanisau, wadda ke dauke da gadaje kusan 240.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Dutse ya ce daga cikin mutum 317 da suka kamu da cutar mutum guda ne ya rage yanzu haka da ba a sallama daga asibiti ba.

Wakilin Freedom Rediyo a Dutse Aminu Umar Shuwajo ya rawaito gwamnan na cewa wannan nasara ta samu ne sakamakon irin hadin kan da mutane suka bayar, da kuma wakilan kwamati dake aiki ba dare ba rana.

Gwamnan a cikin jawabin nasa ya kuma ja hankalin shugabannin ‘yan kasuwa game da bin ka’idojin da aka gindaya kafin a bude kasuwanni, tare da gargadin cewa akasin hakan zai sanya gwamnati ta rufe kasuwannin da aka samu da sabawa doka.

Gwamnatin ta Jigawa ta ce zata bude sashen daukar gwajin cutar corona manyan asibitocin da ke fadin jihar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 328,732 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!