Labarai
Hanyar jirgin kasa: Buhari ya mai da jihohin arewa maso gabas saniyar ware – Gwamnan Gombe
Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce, gwamnatin tarayya ta mai da yanki arewa maso gabas saniyar ware, a ayyukan sabunta titunan jirgin kasa da ke ci gaba da wakana a sassa daban-daban na kasar nan.
Gwamnan na Gombe ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke tattaunawa da karamar ministar sifiri Gbemisola Rukayyat Saraki wadda ta kai masa ziyara gidan gwamnati a jiya alhamis.
Ya ce, titin layin dogo da ya hada jihohn arewa maso gabas, musamman na Maiduguri zuwa Gombe har ya kai ga Fatakwal an ki mai da hankali akansa duk kuwa da irin gudunmawa da ya ke bayarwa wajen bunkasa tattalin arzikin yankin.
Muhammad Inuwa Yahaya ya kara da cewa, idan har aikin shimfida layin dogo zai kai har ga Maradi a jamhuriyar Nijar, bai ga dalilin da zai sa kuma yankin arewa maso yammaci a mai da shi saniyar ware ba.
Wakiliyar mu Aisha Baba ta ruwaito gwamnan na yin kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta fara aikin layin dogon Maiduguri zuwa Fatakwal don bai wa al’ummomin yankin damar amfana da aikin sabunta layin dogon.
You must be logged in to post a comment Login