Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Matsalar Tsaro: Ba na iya bacci da ido biyu – Gwamnan Gombe

Published

on


Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce, ba ya iya bacci idon sa a rufe sakamakon tabarbarewar tsaro a yankin jihohin arewa maso gabashin kasar nan.

Gwamnan na Gombe ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke jawabi a wajen bikin yaye wasu dakaru na musamman a cibiyar nazarin harkokin tsaro da ke Bwari a birnin tarayya Abuja.

‘‘Idan na ce da ku ina iya rufe idanu na in yi bacci da daddare to gaskiya wasa na ke yi, saboda halin tabarbarewar tsaro ya sanya bana iya bacci’’

‘‘Saboda haka halin da ake ciki abin damuwa ne kuma abin takaici wanda ke bukatar hadin kan dukkan nin masu ruwa da tsaki’’

‘‘Dole ne mu rika aiki tukuru wajen hadin gwiwa da kowane bangare don dakile matsalar da ke gaban mu’’ a cewar gwamnan na Gombe.

Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya ya kuma ce dole a rika alakanta rashin tsaro a kasar nan da halin da ake ciki a yankin Sahel da na kudu da hamadar Sahara da ma duniya baki daya, domin bazuwar makamai daga kasar Libya da Mali ya taka rawa gaya wajen kara ta’azzara halin da kasar nan ke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!